fbpx
Wednesday, June 29
Shadow

Shugaba Muhammadu Buhari ya gana da firaym Minista na kasar Jamaica

Shugaban kasar Najeriya, mejo janar Muhammadu Buhari ya gana da firaym minista na kasar Jamaica, Andrew Holness akan batun taron shuwagabanni ma mulkin mallaka karo na 26.

Inda shugaba Buhari ya bayyana cewa akwai alaka mai karfi tsakanin Najeriya da Jamaica, kuma yana godiya bisa taimakon da suke baiwa Najeriya ta fannin siyasa da kuma tattalin arziki.

Inda shima firaym Ministan, Andrew Holness yace Najeriya na taimakawa Jamaica sosai kuma yanzu haka akwai yarjejeniyar kasuwanci a tsakaninsu.

Sun gudanar da wannan taron ne a Kigali dake kasar Ruwanda ranar alhamis.

Leave a Reply

Your email address will not be published.