Shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari ya jinjinwa tawagar ‘yan wasan kwallon kafa ta mata duk da an cire su a gasar kofin Afrika ta mata wato WAFCON.
Hadimin shugaban kasar, Femi Adesina ne ya bayyana hakan yayin da shima ministan wasanni Dare ya jinjina masu.
Tawagar Super Falcons din tayi kokari sosai a wasan domin jan kati biyu ta samu amma duk da haka sai a bugun fenariti Morocco taci su 5-4 bayan su tashi wasa daci 1-1.
Wanda hakan yasa burin tawagar na lashe kofin karo na goma ya samu cikas saida kuma a gasar mai zuwa.