Shugaban kasar Najeriya, mejo janar Muhammadu Buhari yayi maraba da zuwan watan Ramadan mai dumbin daraja da alfarma.
Ramadan ya kasance wata mai alfarma kuma mai albarka wanda musulmai suke azumta, kuma yana kara masu kusance da tsron mahaliccin su wato Allahu Subhanahu Wata’ala.
Inda shima Shugaba Buhari ya taya yan uwa musulmai na fadin duniya murnar shiga watan mai alfarma, kuma ya bukaci musulmai masu arziki cewa suyi kokari wurin ciyar da marasa karfi a wannan watan mai albarka.