Wani babban dan Boko Haram da Sojoji suka kama a jihar Borno me suna Abdulkadir Abubakar wanda yanawa kungiyar Boko Haram din aikin leken aisiri, ya bayyana cewa shugaban Boko Haram din, Abubakar Shekau yazu haka a karye yake, duk da dai cewa be bayyana dalilin karayar ta shekau dinba amma yace Allah ne ya kamashi saboda irin zalincin da yakewa mutane.
Abubakar dake magana a matsayi tubabbe, wanda yayi nadama, yace duk irin amfani da Shekau din yake da ‘yan mata, yara kanana yana turasu suna kashe kansu ta hanyar kunar bakin wake bai kamataba, haka kuma yayi kira ga sauran ‘yan boko Haram din da suka ware daga Shekau suka kafa nasu kungiyoyin dasu watsar da wannan akida domin bamai kaiwa gaci bace, kamar yanda jaridar Sunnews ta ruwaito.
Abubakar ya kara da cewa da yawa da suka fita daga karkashin Shekau suka kafa tasu kungiyar na adawa da irin yanda yake gudanar da al’amura saboda tsaurinshi yayi yawa, za’a cemai ga yara da mata can yunwa na damunsu a sansanin ‘yan boko haram din amma sai yace ba hakkinshi bane ya ciyar dasu, wata rana ma da wani yamai magana saida ya kasheshi, wannan dalilin yasa wasu suka ware daga cikinshi harma suke yakarshi.
Abubakar ya kara da cewa abinda suke yi ba daidai bane, kuma duk wandama yake jin dadi a zuciyarshi akan irin yanda suke kashe mutane to shima sai Allah ya hukuntashi, a karshe yayi kira ga ‘yan Boko Haram din su rungumi zaman lafiya su ajiye makamai.