fbpx
Monday, August 15
Shadow

Shugaban Buhari yayi tsokaci kan gargadin da hukumar DSS tayi mai na tsayar da Musulmai da APC tayi a matsayin ‘yan takararta ma shugaban kasa

Shugabam kasar Najeriya Muhammad Buhari yayi tsokaci akan gargadin da hukumar DSS tayi mai bayan APC ta tsayar da musulmai a matsayin ‘yan takararta na shugaban kasa.

Inda hukumar tace masa wannan zabin da APC tayi na Tinubu da Shettima zai iya haddasa fada a kasar tsakanin Musulmai da Kirista.

Amma yanzu shugaban kasar ya bayyana cewa shi ba wanda ya nemi shawarar shi kan zabar musulmi da Tinubu yayi a matsayin abokin takararsa.

Hadimin shugaba Buhari, Garba Shehu ne ya bayyana hakan bayan hukumar ta gargadi shugaban kasar yau juma’a.

Leave a Reply

Your email address will not be published.