fbpx
Tuesday, September 29
Shadow

shugaban Bundlesliga: Tafiyar Haaland zuwa Real Madrid ci bayane a garemu

Kungiyar Real Madrid da PSG suna harin siyan tauraron Dortmund saboda Haaland yana kokari sosai a wannan kakar wasan. Seifert ya tattauna da MARCA a karo na farko tunda aka cigaba da buga wasannin Bundlesliga.

Marca sun tambaya Seifert cewa shin yana jin dadi kasancewar sune suka fara cigaba da buga wasanni kwallon kafa?, sai yace baya tunani sosai akan hakan, amma burin shi shine ya jagoranci tafiyar cigaba da buga wasannin kwallon kafan duk da cewa sun samu korafe korafe daga bakin duniya. Amma kuma duk da hakan yawancin sauran gasar nahiyar turai suna da ra’yin bin tsarin su, kuma hakan babbar girmamawa ce.

Sun kara tambayar Seifert cewa shin idan Haaland ya koma Madrid, Bundlesliga zasu yi babban rashi, sai yace duk wani babban dan wasan daya tafi to ci baya ne, shin idan ya san shi kwararren dan wasa ne me ya kawo shi Dortmund? Marca: saboda Dortmund sun hanzarta kuma sunyi kokari wajen siyan shi.

 

Seifert: ku kuka ce hakan ba ni ba. Abu me sauki ne neman dan wasan daya zamo fitacce a duniya, amma babban abun shine siyan dan wasan kafin duniya ta san shi kuma Dortmund sun yi hakan saboda sun siye Haaland tun kafin mayan kungiyoyin nahiyar turai su fara neman shi.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=hdlabarai.aplibwxLeave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *