fbpx
Thursday, August 18
Shadow

Shugaban Dortmund ya gargadi Manchester United cewa basa su rage masu farashin da suka sawa jadon sancho ba

Shugaban Dortmund Hans-Joachim Watze ya gargadi Manchester United cewa basa su taba rage masu farashin da suka sawa jadon sancho ba a kakar wasan bana duk da cewa annobar cutar coronavirus tasa an rage farashin yan wasan kwallon kafa.

 

 

Watze ya Kara da cewa tun kafin barkewar cutar coronavirus dama Dortmund sun fi so sancho ya cigaba da wasa a kungiyar su.
Dan wasan ingilan yana kokari sosai a kakar wasan bana, yaci kwallaye 17 kuma ya taimaka wurin cin kwallaye har guda 19 a wasanni guda 35 daya buga a kakar wasan bana. United na shirin mayar da sancho dan wasa mafi tsada a ingila don sun taya shi a farashin euros miliyan 100.
An samu labari cewa Dortmund sun yankewa sancho farashin euros miliyan 120 kuma ana sa ran cewa kungiyar Chelsea da United zasu iya siyan dan wasan dan su karawa kungiyoyin su karfi.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Karanta wannan  Da Dumi Duminsa: Elon Musk zai saya kungiyar Manchester United

Leave a Reply

Your email address will not be published.