fbpx
Thursday, July 7
Shadow

Shugaban kamfanin BUA ya bayar da tallafin Naira miliyan 100 ga jihar Kwara

Shugaban Kamfanin BUA, Alhaji Abdulsamad Rabiu ya ba da gudummawar  Naira Miliyan 100 ga asusun bada tallafi kan yaki da cutar Corona na jihar Kwara.

 
 
Tallafin yazo ne ‘yan makonni bayan da ya bada tallafin biliyan 1 ga wasu jihohin ciki hadda kwara, haka zalika ya bada makamancin wannan tallafin ga gwamnatin tarayya har Naira biliyan 1 tare da karin biliyan 3.3 ga jihohin kano da legas duk dan yaki da cutar Covid-19.
 
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da aka fitar a Ilorin a ranar Alhamis wacce Babban sakataren yada labarai ya rattaba hannu ga gwamna Abdulrahman Abdulrasaq da mai magana da yawun jihar Covid-19, Mr. Rafiu Ajakaye.
 
Sanarwar tace a sakamakon tallafin yanzu jihar ta samu jimlar kudi Naira miliyan N230m wanda zai taimaka wajan yaki da cutar.
Gwamnatin jihar ta godewa Dan kasuwar bisa tallafin da ya bayar tare da godiya shauran wanda suma suka bada tasu gudun mawar.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.