Shugaban karamar hukumar Kalgo A jihar Kebbi, Alhaji Samsu Umar Faruk ya kai kayan agaji da kudi zuwa ga wadanda ambaliyar ruwa ta shafa kwanakin baya a jihar.
A cewarsa, ya kai taimakon ne domin ragewa al’ummomin da Ambaliyar ruwan ta shafa a yankin wahal-halu.
Ya bayyana cewa sama da gidaje 156 ne ambaliyar ta lalata, a garuruwan Kalgo, Kirishi da Badariya.
Fiye da mutane 60 da abin ya shafa za suci gajiyar tallafin kudi a Badariya yayin da mutane 96 za su amfana a garin Kalgo da kirishi da tallafin kudi naira dubu 14 ko wanan su.
Hakimin Kalgo, Alhaji Haruna Bashar, ya yaba da gudunmawar da a ka baiwa al’ummar karamar hukumar.