fbpx
Thursday, August 18
Shadow

Shugaban kasa Buhari yayi addu’ar samun sauki ga Mai martaba Sarkin Daura

A jiya ne Shugaba Muhammadu Buhari yayi addu’ar samun sauki ga Mai martaba Sarkin Daura, Alhaji Umar Farouk Umar, bayan an garzaya da shi babban asibitin tarayya dake jihar Katsina. Buhari.

 

Hakan na zuwa ne ta cikin wata sanarwa daga mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu, ya aike zuwa ga sarkin Daura tare da fatan alheri da addu’o’i ga Sarkin.

Shugaba Buhari ya ce ‘ya samu labarin rashin lafiyar sarki ba zato ba tsammani inda yayi masa fatan alheri tare da addu’ar samun sauki cikin gaggawa.

Karanta wannan  Shugaba Buhari ya nada Aliko Dangote a matsayin shugaban sabuwar kungiyar da zata kawo karshen cutar Malaria a Najeriya

An dai garzaya da sarkin Daura zuwa asbiti ne dake jihar katsina a sakamakon hawan jini.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.