A yau Juma’ane shugaban kasa Muhammadu Buhari ga mataimakinshi farfesa Yemi Osinbajo tare da wasu ministoci suka gana da shuwagabanin addinan Musulunci dana kirista a fadar shugaban kasar, a lokacin ziyarar tasu shugaba Buhari yayi alkawarin gyara sukar da akewa gwamnatinshi na cewa ta bayar da mukamai ga ‘yan Arewa fiye da ‘yan kudu.
Ya kara da cewa ya bayar da umarnin a kawomai sunayen shuwagabannin ma’aikatan dake rike da manyan ma’aikatun gwamnatin nashi dan ya duba yayi gayaran daya kamata.
Haka shugaba Buhari yayi alkawarin ganin ya kula da bangaren shari’a da kuma jami’an tsaro dan ganin an samu zaman lafiya me dorewa a kasarnan.