Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya gana da gwamnonin APC a babban birnin tarayya, Abuja.
An yi ganawar ne a fadar shugaban kasar saidai gwamnonin sun ki cewa komai bayan taron.
Amma ana tsammanin taron bashi rasa nasaba da fitar da mataimakin Bola Tinubu da zasu yi takarar shugaban kasa tare.