Sunday, June 7
Shadow

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umarci Sojojin Najeriya da su hada hannu da ‘yan sanda domin dakile ayyukan yan bindiga da ke haifar da hargitsi a wasu sassan kasar

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bada umarninne ga Sojojin Najeriya da su hada hannu da ‘yan sanda domin dakile‘ ayyukan yan bindiga da ke haifar da hargitsi a wasu sassan kasar.

Umurnin Shugaban yazo ne bayan wasu hare hare da suka faru kwanannan a sassan Sakkwato da Filato inda aka ruwaito mutane 22 da kuma mutum 10 sun mutu a jihohin biyu.

Umarnin ya fito ne a cikin wata sanarwa da babban mai taimakawa shugaban kasa na musamman kan harkokin yada labarai Mallam Garba Shehu ya fitar ranar Juma’a.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umarci Sojojin Najeriya da su hada karfi da‘ yan sanda tare da fatattakar ‘yan fashi daga dazuzzukan da ke kasar nan, musamman a wuraren da suka sha fama da hare-hare kwanan nan.

Shugaban kasan ya ba da umarnin ne a game da kisan mutane 22 a jihar Sakkwato, wadanda ‘yan bindigar sukai tare da rahoton kashe wasu mutane 10 a karamar hukumar Bassa ta jihar Filato.

Biyo bayan umarnin tuni Shugaban Hafsin Sojojin, Lt-Gen Tukur Buratai ya yi magana da Janar din Rundunar Sojoji na jihohin da abin ya shafa, kana ya ba su umarnin karfafa ayyuka da ‘yan sanda don gano yan bindigar domin su fuskanci hukunci.

A karshe shugaban kasa ya nemi da jihohin su taimakawa gwamnatin tarayya wajan magance matsalar, ya kuma jajantawa yan uwan wadan da abun ya shafa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=hdlabarai.aplibwxLeave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *