Shugaban kasar Najeriya, Mejo janar Muhammadu Buhari ya yiwa mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo addu’ar samun sauki bayan an yi masa tiyata.
Hadimin shugaban kasa Femi Adesina ne ya bayyana hakan, inda yace shugaban kasar ya jinjinawa likitocin asibitin Duchess na Legas da sukayi tiyatar.
A jiya asabar ne aka yiwa Osinbajo tiyatar a kafarsa kuma an kammala yayin da zasu sallame shi cikin kwanakin nan.