Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana yace yana alfarin cewa ya bar tarihin yaki da cin hanci da rashawa amma ya yafewa shuwagabannin da suka sace kudin kasa.
A jiya shugaban kasar ya bayyana hakan a ranar yaki da cin hanci da rashawa ta wannan shekarar, inda yace bama Najeriya kadai ba har Afrika bakidaya ba zai bari ayi cin hanci ba.
Amma shugaban kasar duk da wannan furucin nasa daya yi a watannin baya ya yafewa manyan barayin da suka sace kudin talakawa a kasar nan.
Watau tsaffin gwamnonin Joshua Dariye da Jolly Nyame wanda aka kulle a gidan yari Kuje saboda biliyoyin nairar da suka sata.