fbpx
Sunday, August 7
Shadow

Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai shilla kasar Laberia don tattaunawa kan matsalar tsaro

Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai shilla kasar Liberia a yau ranar talata inda zai yi bayanai kan matsalar tsaron da ake fama dashi a yammacin Afrika da kuma bin dokoki.

Shugaban kasar zai ziyarci Monrovia ne a kasar ta Laberia domin tayata murnar cika shekara 175 da samun yancin kai, kuma itace kasar Afrika data dade da samun ‘yanci fiye da kowace kasa a Nahiyar.

Hadimin shugaban kasar Garba Shehu ne zai bayyana a shafinsa na Twitter ranar litinin,

Kuma yace shugaba Buhari ne babban bako a taron bikin murnar zagayowar ramar samun ‘yancin da kasar Laberia zata gudanar.

Leave a Reply

Your email address will not be published.