Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyanawa alkalan Najeriya cewa zasu sha jar miya kafin ya sauka a mulikin kasar nan.
Shugaban ya bayyana hakan ne a fadarsa ranar alhamis din data gabata a watan Yuli.
Inda yace zai yi kokari ya tabbatar da hakan duk da halin da Najeriya ke ciki na rashin tattalin arziki da kuma matsalar tsaron da ake fama dashi a kasar.
Inda yace alkalai nada matukar muhimmanci saboda haka bai kamata a bar su haka nan ba.