fbpx
Monday, August 8
Shadow

Shugaban kasar Amurka, Donald Trump na son a hukunta China saboda yada cutar Coronavirus/COVID-19 a Duniya

Shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya nemi kwamitin majalisar Dinkin Duniya da ya hukunta kasar China saboda zargin da yayi cewa kasar da gangan ta bar cutar Coronavirus/COVID-19 ta shiga Duniya.

 

Ya bayyana hakane a bayanin da ya gabatar a wajan taron majalisar dinkin Duniya inda kasashe ke gabatar da bayanai ta kafafen sada sumunta.

Trump yace China da hafin gwiwar kungiyar Lafiya ta Duniya, WHO sun taimaka wajan yaduwar cutar.

 

Yace WHO da farko tace mutum ba zai iya yadawa wani ba cutar amma ta karyata kanta sannan kuma daga baya tace wanda ya kamu da cutar amma alamunta basu bayyana ba a jikinsa shima ba zai iya yada cutar ba wanda shima daga baya ta karyata kanta.

Karanta wannan  Hukumar 'yan sanda ta damke wani matashi dayake yaudarar 'yan mata yana masu sata a jihar Legas

 

Yace wannan lamari ba abin wasa bane. Saisai kamfanin dillancin labaran AFP ya bayyana cewa shugaban kasar na neman wanda zai dorawa laifine bayan da yayi abinda bai kamata ba wajan kin baiwa cutar kulawa a kasar amurka wanda hakan ya kai ga Mutuwar dubban mutane.

 

Hakanan ana zargin Trump da amfani da wannan dama wajan samun karbuwa a wajan mutanen kasar Amurka saboda gabatowar zabe.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.