Shugaban kasar Amurka Donald J. Trump ya nanata wani sakon nuna cin zarafi da wata kungiyar masu tsattsauran ra’ayin kasar Ingila me suna Ingilace farko, sakon da kungiyar ta wallafa a dandalinta na sada zumunta da muhawara wanda ke dauke da wasu bidiyo dake nuna wasu mutane da ake kyautata zaton musulmaine sun kashe wani yaro sannan sun farwa wani nakasasshe kuma sun ruguza wani mutum-mutumi na kirista.
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Donald Trump ya sake maimaita wannan sako a dandalinshi wanda hakan yake nuna cewa yana goyon bayan waccan kungiya, to saidai hakan be yiwa mutanen kasar, dama wasu na kasashen waje dadiba.
An bayyana saka wannan sako da Trump yayi a dandalinshi a matsayin goyon bayan cin zarafin musulmi da nuna kiyayya garesu.
Firaiministar Ingila Theresa May ta hannun me magana da yawunta tace bai kamata Trump ya wallafa wannan sako dake nuna kiyayya ga musulmai ba.
Amma maimakon ya saduda, sai Trump ya mayar mata da martani cewa kamata yayi ta mayar da hankali kan akidojin musulmai na ta’addanci dake barazana ga faruwar kasarta maimakon sukarshi.
Da yawa dai, musulmai da wadanda ba musulmai ba sunyi Allah wadai da wannan abu da Trump yayi.
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});