fbpx
Wednesday, August 10
Shadow

Shugaban kasar Argentina, Alberto Fernandez ya bukaci Messi yayi ritaya a Newell’s Old Boys

Shugaban kasar Argentina, Alberto Fernandez ya bukaci Messi ya koma kasar shi domin dan wasan yayi ritaya a mahaifar shi. Tauraron dan wasan Barcelonan ya dauki tsawon wasu shekaru a kungiyar Newell’s Old Boys dake garin Rosario kafin ya koma nahiyar turai da aiki.

Fernandez ya bayyanawa C5N cewa Messi yana cikin zuciyoyin su kuma har yanzu basu samu damar kallon shi yana buga a kasar su ba, saboda haka suna so yayi masu alfarma yayi ritaya daga wasan kwallon kafa a kungiyar Newell’s Old Boys. Shugaban Argentinan ya kara da cewa idan har Messi bai yi ritaya a Barcelona to a Newell’s Old Boys ya kamata yayi ritaya kamar yadda Marcelo Bielsa yayi.
An tambaya shugaban kasar cewa ya zabi gwanin shi tsakanin Messi da Maradona, sai Fernandez yace Maradona dan wasa ne wanda ya gagari duniya bakidaya kuma bai taba ganin wani dan wasa kamar shi ba. shugaban ya kara da cewa yana son Maradona sosai fiye da yadda yake son Messi kuma dalili shine saboda shi ya taso ne a kungiyar Argentinos.
Fernendez yace yana kallon yadda Maradona yake fafatawa da duniya bakidaya a wasannin kwallon kafa saboda shi gwarzo ne sannan yana da karfi sosai.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.