Rahotanni daga kasar Burundi sun nuna cewa cutar Coronavirus/COVID-19 ce ta kashe shugaban kasar, Pierre Nkurunziza.
A ranar 9 ga watan Yuni ne hukumomin kasar suka bayyana cewa cutar bugun zuciya ta kashe shugaban kasar a farat daya.
Saidai wata majiya ta Asibitin da aka kaishi na Karusi ta gayawa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa cutar Coronavirus/COVID-19 ce ta kashe shugaban.
Hakan ya farune bayan da matar shugaban kasar ta kamu da cutar a baya kuma ranar 30 ga watan Mayu aka dauketa zuwa kasar Kenya dan dubata.
Majiyat Asitin tace an je da shugaban kasar aka kuma bukaci su bada abin taimakawa Numfashi wanda shi kadaine tilo suke dashi a Asibitin amma ashe tuni shugaban kasar ya mutu.