fbpx
Wednesday, October 21
Shadow

Shugaban kungiyar (NURTW) reshen jihar Yobe, Alhaji Bulama Kaku Ali ya roki gwamnatin tarayya da ta jihohi da su gyara titunan kasar nan.

Shugaban kungiyar ma’aikatan sufuri na kasa (NURTW) reshen jihar Yobe, Alhaji Bulama Kaku Ali ya roki gwamnatin tarayya da ta jihohi da su gyara titunan kasar nan.

A cewarsa a cikin kaso 10 kaso bakwai na manyan hadarurruka na faruwa ne sakamakon rashin kyawun tituna.

Dan haka ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta jihohi da su duba yanayin titunan kasar domin gyaran su.

Shugaban ya yi kiran ne yayin da yake zantawa da manema labarai a ofishinsa da ke Damaturu.

Hakanan Shugaban ya gargadi direbobi da su guji tukin ganganci da wuce gona da iri, lura da cewa irin wadannan halayen na haifar da hadari inda mutane ke salwantar da rayukansu da dukiyoyinsu.

 

 

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=hdlabarai.aplibwxLeave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *