SHUGABAN KUNGIYAR TINUBU A SOKOTO YA SAUYA SHEKA DAGA JAM’IYYAR APC ZUWA JAM’IYYAR PDP
Daya Daga cikin dattijawa kuma tsohon dan siyasa, kuma hamshakin dan kasuwa wanda shine shugaban babbar kungiyar yakin neman zaben Bola Ahmed Tinubu anan Sokoto mai suna Alhaji Usman Shehu Bature Gidan Madi ya sauya sheka daga jam’iyyar APC zuwa jam’iyya mai farinjini da albarka ta PDP.

Shugaban jam’iyyar PDP na jaha, Hon Bello Aliyu Goronyo, Daraktan yakin neman zaben Gwamna, Alhaji Yusuf Suleiman (Dan Amar Sokoto) Kwamishina mai kula da ma’aikatar lamurran watsa labarai, Hon. Akibu Dalhatu, Shugaban hukumar jindadin alhazzai, Alhaji Mukhtar Maigona, Kodineta na yakin neman zabe na karamar hukumar mulki ta Tangaza, Hon Ibrahim Garba Wakaso, Mataimakin Sakataren jam’iyya yankin tsakiyya, Alhaji Mustapha Lanas Gidadawa duk sun shedi karbar shi.
Abu Gbow
#MSU #MallamUbandoma #BafadenAllaah #MSU4G
#UbandomaSagir #GaAllaahMukaDogara #MalUbandomaAlheriNe #SokSaiMal