Monday, March 30
Shadow

Shugaban ma’aikatan Buhari, Abba Kyari ya kamu da Coronavirus/COVID-19 saidai NCDC ta yi magana

Rahotannin dake fitowa daga fadar shugaban kasa na cewa shugaban ma’aikata na fadar shugaban kasar, Abba Kyari ya kamu da cutar Coronavirus/COVID-19.

 

Rahoton yace Abba kyari yayi gwani kuma gwajin ya nuna cewa yana dauke da cutar kamar yanda Thisday ta ruwaito.

 

Dalilin hakane yasa aka gwada Shugaban kasa,Muhammadu Buhari shima akan cutar inda shi kuma sakamakon ya nuna cewa bashi da ita.

 

Abba Kyari yayi tafiya zuwa kasar Jamus a ranar Asabar, 7 ga watan Maris inda ya gana da wasu kamfanonin kan habaka wutar Najeriya.

 

Saidai da Daily Post ta tambayi hukumar kula da cututtuka ta Najeriya, NCDC tace bata fitar da sanarwar cutar akan mutum daya sai ta tsaya ta yi bincike tukuna sannan kuma bata bayar da sunayen mutanen da suka kamu da cutar.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=hdlabarai.aplibwx

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *