Amaju Pinnick, shugaban hukumar kwallon kafa ta Najeriya (NFF), ba zai nemi shugabancin kungiyar a karo na uku duk da cewa wa’adin mulkinsa zai kare a watan Satumba 2022.
Wannan na zuwa ne bayan matsin lamba daga mutane da yawa suna kira ga Pinnick ya yi murabus sakamakon gazawar Najeriya na samu tikitin shiga gasar cin kofin duniya ta 2022.
Mista Pinnick, a ranar Juma’a 8 ga watan Afrilu, ya bayyana ra’ayinsa kan cewa zai tsaya takarar neman mukamin babban hukumar NFF a karo na uku, yayin da ya amince cewa shigarsa a harkokin kwallon kafa a tsawon shekaru ya yi wa iyalinsa mummunar illa.
Da yake magana a gidan talabijin na Arise TV, ya ce : “Abin ya kasance tashin hankali sosai ga kwallon kafa ta Najeriya. Na cancanci yin takara bisa ga ƙa’idodi.
Yace ba zai tsaya takarar ba saboda iyalinsa sun bukaci hakan, kuma sunce yayi iya kokarinsa dan haka akwai bukatar yabar wajen.