fbpx
Tuesday, August 9
Shadow

Shugaban Real Madrid, Florentino Perez yayi magana kan Mbappe da Pogba

Kungiyar Real Madrid taci kofin La Liga kari na 34 a gida tsakanin ta da kungiyar Villarreal wanda suka yi nasarar tashi biyu da daya kuma Benzema ne yaci masu gabadaya kwallayen.

Ana sa ran cewa kungiyar zakarun gasar La Ligan zata kashe makudan kudade idan aka bude kasuwar yan wasan kwallon kafa musammam wurin siyan yan wasan da suke hari, kamar tauraron Paris Saint German Mbappe da dan wasan United Paul Pogba.

Amma sai dai shugaban kungiyar Florentino Perez ya bayyana cewa kungiyar shi baza ta siya wani dan wasa ba a wannan kakar wasan saboda annobar korona ta dakile hanyoyin samun kudin wasan kwallon kafa.

Perez ya gayawa El transistor cewa halin da ake ciki na yanzu yayi muni sosai. Kuma mawuyacin abu ne acewa yan wasa su karbi ragin albashi domin a siyo wani dan wasa, saboda haka Madrid zata jinkirta kuma zata siya kwarrarren dan wasa idan aka samu canjin yanayi.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.