Shugaban sojojin Najeriya, Maj Gen I Attahiru ya tafi jihar Borno saboda hare-haren da Boko Haram suka kai a daren Juma’a akan wasu garuruwan jihar.
Rahotanni sun bayyana cewa Boko Haram sun kwace wasu garuruwa 2 bayan fafatawa da sojojin Najeriya.
Ana tsammanin shugaban Sojin zai gana da kwamandojin dake jagorantar yaki da Boko Haram din.