fbpx
Wednesday, August 10
Shadow

Shugaban ‘yansandan Najeriya ya Bukaci a kwato makaman da suka saba ka’ida a hannayen mutane

Shugaban ‘yansandan Najeriya, IGP Muhammad Adamu ya bukaci da a kwato makaman da suka saba ka’ida dake hannayen Mutane.

 

Sanarwar da kakakin Rundunar ‘yansandan, Frank Mba ya bayyanawa manema labarai ta ce an bukaci kwamishinonin ‘yansanda su tabbatar an aiwatar da wannan umarni. Hutudole ya samo muku cewa sanarwar ta nemi kuma a zauna da kungiyoyin ‘yan Banga dan ganin suna aiki bisa doka.

Hakan na zuwane yayin da Rundunar ‘yansanda ta bayyana cewa kungiyoyi da dama na sayen Makamai ta hanyar da bata dace ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published.