Kwamishinan ‘yansandan jihar, Idrisu Dauda ne ya mikawa iyalan mamatan kudin ta hanyar cek.
Da yake mikawa iyalan kudin su 20 a madadin shugaban ‘yansandan, Usman Baba, yace wannan daya daga cikin tsarin inshora ne na tallafawa iyalan ‘yansandan.
Ya baiwa iyalan shawarar cewa, su yi amfani da kudaden ta hanyar data dace.
Ya kuma godewa shugaban ‘yansandan kan wannan mataki na tallafawa iyalan ‘yansandan da suka mutu.