fbpx
Monday, August 3
Shadow

Shugabannin kasa da aka samu daga Arewa ne suka hana Najeriya ci gaba: Babu Mahalukin da ya isa hana Tinubu Takara>>Babacir Lawal

Tsohon sakataren gwamnatin tarayya,  Babachir Lawal ya bayyana cewa babu wanda ya isa ya hana Bola Ahmad Tinubu takarar shugaban kasa jam’iyyar APC a shekarar 2023.

 

Ya bayyana hakane a hirar da yayi da Punch inda ya kara da cewa, wasu gwamnonin APC da gangan suke kokarin rura wutar rikicin jam’iyyar dan cimma manufarsu.

Yace abin na bashi dariya saboda wanda suka yi kutun-kutun din cire Adams Oshiomhole daga shugaban jam’iyyar na tunanin zasu iya hana Tinubu takarar shugaban kasane.

 

Yace babu wani me tunani na kwarai da zai yi yunkurin hana Tinubu takarar shugaban kasa a 2023. Yace kai bama Tinubu ba, koma wanene ya kamata a barshi ya tsaya takara idan yana da ra’ayi.

 

Yace ya kamata a girmama alkawarin da aka yi, shugaban kasa a 2023 ya fito daga kudu, yankin Yarbawa.

 

Yace da ake ta maganar sai dan Arewa yayi shugabanci, tun da Abacha ya mutu a kasarnan ba’a zauna lafiya ba, daga matsalar tsaro zuwa matsalar tattalin arziki.

 

Yace kai shuwagabannin da aka yi daga Arewane suka zamarwa Najeriya matsalar da ta kasa ci gaba.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=hdlabarai.aplibwxLeave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *