fbpx
Wednesday, February 24
Shadow

Shugabannin kungiyar kwalan kafa ta kano Pillars sun yi barazanar sallamar ‘yan wasan da basa taka leda a kungiyar

Shugaban kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars, Surajo Shuaibu ya ce duk wani dan wasan da ba ya taka leda a kungiyar ya kamata ya fara shirin barin kungiyar ko kuma a mayar da shi karamar kungiyar.

shugaban ya bayyana hakan ne a yayin da yake zantawa da manema labarai a ranar Laraba a Kano kan rawar da suka taka a gasar Firimiyar Nigeria da ke gudana.

A cewarsa, a yanzu, kungiyar tana tsammanin dan wasan gaba daga Kamaru wanda ke son taka leda a kungiyar, ya kara da cewa kulob din yana taka rawar gani a gasar da ke gudana.

Mista Shuaibu ya bayyana cewa daga cikin wasanni 38, ya zuwa yanzu kungiyar ta buga wasanni 10, ta yi nasara a wasanni shida, ta yi rashin nasara a wasanni biyu sannan ta kammala wasanni biyu da kunnen doki.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *