Shugaban sanatoci da sauran manyan yan takarar majalisa na jam’iyyar APC na cikin babbar matsala bayan da jam’iyyar taki mikawa INEC sunayen yan takararta na majalisar tarayya akan lokaci.
Hukunar zabe ta bayyana ranar 17 ga watan yuni a matsayin rana ta karshe da jam’iyyu zasu mika mata sunayen amma APC bata bayar da nata ba.
Sai dai manema labarai na Sahara sun bayyana cewa jigajigan jam’iyyar ta APC sunce zasu gana da hukumar zaben yau ranar talata.
Yayin da suke fatan zata amince ta kara wannan wa’adin data sakawa jam’iyyu su bayyana mata sunayen ‘yan takarar nasu.