fbpx
Wednesday, July 6
Shadow

Sifofin mace mafi Alkhairi a cikin mata “Inji Sayyadi Ali (AS)

Sifofin mace mafi Alkhairi a cikin mata
“Inji Sayyadi Ali (AS)

1-tana yarda da hukuncin ubangijinta,

2-tana shiryatar da mijinta zuwa ga aikata alkhairi,

3-bata fita daga gidanta fita Maras dalili, na hankali,

4-tana yin salloli 5 na wuni akan lokaci,

5-bata yada sirrinta dana mijinta,

6-ba’a kallon takalminta, ba’a jiyo sautinta daga cikin gidanta, ko akan hanya in tana tafiya,

7-wasu basu kallon sifarta sai mijinta, mai buwayaa ce gidansu, mai kaskantar da kanta ce a gaban mijinta,

8-mai shayarwa ce ga yaranta, ita din aljannar mijinta ce a cikin gidanta,

9-in tasamu abinda take bukata a gun mijinta sai tayi godiya garesa,

10-in bata samu ba saboda yanayi sai tayi hakuri batare da ta tasar mishi da hankali ba,

11-in yashigo gida zuwa gareta, tanayin farin ciki, tasanyashi farin ciki, tana bayyanar da annurin fuskarta cikin murmushi zuwa gareshi,

Karanta wannan  Na gaji da daukar nauyin kaina aure nake nayi, cewar tauraruwar Nollywood

12-in ya fita daga gidan tana damuwa, saboda tsananin shaukinta gareshi,

13-in yayi mata kuskure tanayin uzuri gareshi, ta hadiye fushinta,

14-in baya gidan tana Kare masa mutuncin kanta,

15-in ta kalli laifuka daga gareshi sai ta lullube sirrinsa,

16-in ya nemi uzuri daga gareta tanayi masa uzuri.

Wadannan kadan ne daga cikin sifofin mafi alkhairin mace a cikin mataye, daga tsattsarkan hareshen imamu Ali (as)

Ko ban tambaya nasan dukkan mazaje munada muradin mallakar ire iren wadannan nagartattu mataye, Allah ya azurtamu dasu.

Allah ya azurta matayan da arzikin wadannan halaye, sannan ya azurtasu Suma da mallakar mazaje nagari.

Daga Alfijir Hausa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.