fbpx
Thursday, September 29
Shadow

Siyasa: Atiku ya aurar da yarinyar Sule Lamido ga jigon APC a jihar Zamfara

Sule Lamido, wanda ya kasance tsohon gwamnan jihar Jigawa kuma jigo a cikin mutanen da suka kirkiri jam’iyyar PDP ya aurar da diyarsa ga jigon APC a jihar Zamfara.

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP Atiku Abubakar ne wakilin Surayya Lamido wadda ta angwance da Yazid Danfulani.

Yazid Danfulani ya kasance kwamishina a karkashin tutar APC a jihar amma duk da haka Lamido ya ajiye batun adawar siyasa a gefe ya aura masa ‘yar cikinsa.

Wanna ba shine karo na farko da manyan jam’iyyun kasar nan suke ajiye batun adawar siyasarsu a gefe su auri junansu ba, kuma hakan yana sawa duk su taru wuri guda suyi raha da junan su.

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published.