fbpx
Thursday, August 18
Shadow

SIYASA BADA GABA BA: Ganduje Ya Taya Kwankwaso Murnar Cika Shekaru 64

Gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya taya tsohon Gwamnan Kano, Injiniya Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso murnar cika shekaru 64 a duniya.

Wanan yana kunshe ne cikin wata sanarwa da aka wallafa a cikin Jaridar Daily Trust, inda Ganduje yake taya Kwankwaso murnar cika shekaru 64.

 

A wannan rana ce madugun Darikar Kwankwasiyya, yake cika shekaru 64 a duniya. Wanda aka fara gudanar da bikin jiya a garin Muntare dake Karamar hukumar Rano a jihar Kano.

 

Bikin zai cigaba a wannan rana tare da bude sabon gidan rediyo mai suna Nasara, duka na daga cikin bangaren bikin nasa na cika shekara 64 a duniya.

Karanta wannan  Da Dumi Duminsa: Gwamnoni zasu gana da shugaba Buhari ranar laraba kan matsalolin kasa musamman tattalin arziki

 

Duk da irin hamayyar siyasar dake tsakanin Kwankwaso da Ganduje hakan bai hana shi taya tsohon mai gidan nasa murna ba.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.