Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya bayyana cewa yana kira ga ‘yan Siyasar Najeriya su fahimci cewa Siyasa ana yin ta ne dan ci gaban kasa ba wai dan fada ba.
Yace yana jawo hankalin duk wanda aka yi zabe aka gama to a hada kai da wanda yayi Nasara dan hadin ci gaban jama’a.
Shugaban ya bayyana hakane a wajan wani taro da aka yi a Bayelsa inda ya jinjinawa gwamnan Jihar, Duoye Diri kan amsar ‘yan Adawa dan a tafi tare.