Daga Nusaiba Taseeu Abdulraheem
Ba za ka ta’ba ganin ‘ya’yan manyan ‘yan siyasar kasar nan sun fito media suna zage-zage kan siyasar ‘iyayensu ba, ba kuma za ka gan su dauke da muggan makamai a taron neman zaben siyasa ba.
Sai kai da ba ka son ciwon kanka ba, don an siya maka wayar da ba ta wuce dubu talatin ba, ka hau Facebook kana zage-zage da ashariya. Ke nan sun mayar da kai Karen farauta?
Su wadanda kake zage-zagen saboda da su sun killace ‘ya’yansu asalima suna auran junansu. Kuma idan suka hadu za ka ga suna faran-faran da juna, a koyaushe dayansu na iya komawa bangaren da kake adawa da shi idan ya ga zai sami mafita.
Don haka talakawa ku san ciwon kanku. Kamata ya yi yadda ake ba ku makamai ku fita kamfen na siyasa ya kasance akwai ‘ya’yansu a ciki.