SÓ GAMÔN JÍNÍ: Bayan Ya Shafé Shékaraú Da Dama Yana Ƙaúnar Hadíza Gabón Yanzú Da Súka Haɗú Ya Kasa Círe Idonsa Daga Kallónta😂
Wannan bawan Allah ɗan Maiduguri ne, wanda ya shafe shekaru da dama yana ƙaunar Hadiza Gabon, irin son da yake mata ya kai matsayin da mutane keyi masa isgili, sukance bata da lokacinsa, dan haka ba zai taɓa ganinta ba.
Kwatsam Sai ga Hadiza Gabon ta sauka garin Maiduguri waje bikin Halima Atete, kwatsam Allah ya haɗa fuskokinsu.
Sun gaisa sosai, sai dai tunda suka haɗu bai kau da ido daga kanta ba, ita kuwa wannan yanayi da ya shiga yayita bata dariya.
A karshe ta bashi lambar wayarta don cigaba da magana nan gaba.
Mé za kúce ?