Sojojin Najeriya 2 ne suka rasa rayukansu sanadiyyar hadarin mota a garin Damba dake jihar Zamfara.
Lamarin ya farune da misalin karfe 11 na safiyar yau inda sojojin ke tafiya cikin zugar motocinsu amma sai aka samu Akasi daya daga cikin motocin sojojin ta kwace ta daki wata motar Golf, kamar yanda wani shedar gani da ido, Anas Damba ya shaidawa Punch.
Yace daya daga cikin sojojin ya fado daga cikin motar inda motar sojin ta takashi, nan take ya mutu. Sauran hudun kuma aka garzaya dasu Asibiti. Daya daga ciki ya mutu a Asibiti.
Me magana da yawun Operation Hadarin Daji, Kaptin Ibrahim Yahaya ya tabbatar da faruwar lamarin.