fbpx
Tuesday, August 9
Shadow

Sojoji 3 sun rasa Ransu a musayar wuta da ‘yan Bindiga a Zamfara

Sojojin Najeriya 3 sun rasa ransu a wata Musayar wuta da suka yi da ‘yan Bindiga a kauyen Kabasa dake karamar hukumar Gusau ta Jihar Zamfara.

 

Mazauna garin sun gayawa Daily Trust cewa, ‘yan Bindiga sun shiga suna ta harbin kan mai uwa da wabi.

 

Lamarin ya farune ranar Talata, kuma bayan sojojin 3, akwai Mutane 7 da suka rasa rayukansu.

 

Gwamnan jihar, Bello Matawalle ya bakin kwamishinan yada labarai, Ibrahim Dosara ya bayyana kaduwa da jin wannan labarin inda yace yana mikawa iyalan wanda aka kashe ta’aziyya.

Karanta wannan  'Yan ta'addan ISWAP sun kai sabon hari a Maiduguri sun kashe dan samda guda

“The whole community was thrown into pandemonium as several other residents trying to escape the attack were injured. Seven people were confirmed dead in the attack,” a resident identified Saminu Usman told Daily Trust.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.