fbpx
Monday, August 8
Shadow

Sojoji 356 na son barin aiki saboda gajiya da Aikin

Rahota ni daga gidan Sojan Najeriya na cewa sojoji 356 na son barin aikin saboda gajiya da aikin wanda hakan na nuni da rashin karfafa gwiwa daga shuwagabannin sojin, kamar yands hutudole ya samo daga Premium times.

 

Majiyar tamu ta bayyana cewa ta samu daga wata majiya daga gidan sojan cewa Sojoji 356 ne keson barin aiki saboda gajiya da aikin sannan kuma akwai 24 dake saon barin aikin saboda karbar sarautun gargajiya.

Tuni dai shugaban sojin, Janar Tukur Yusuf Buratai ya amince da barin aikin sojojin.

Karanta wannan  Hallau rundunar sojin sama ta sake kashe shugaban 'yan ta'addan jihar Katsina tare da tawagarsa

 

Majiyar tace akwai kuma wasu sojoji  da suka wugar da bindigunsu da kakinsu suka tsere saboda gajiya da aikin.

 

Saidai me magana da yawun hukumar Sojin Majo Sagir Musa yace wannan labari ba gaskiya bane, yace akwai karfin gwiwa sosai tare da sojojin Nakeriya.

 

Yace kuma Sojojin na aikie kyau wajan yaki da matsalolin tsaro a sassa daban-daban na kasarnan.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.