fbpx
Wednesday, July 15
Shadow

Sojoji 47 ne Boko Haram suka kashe mana>>Rundunar sojin Najeriya

Hukumar sojin Najeriya ta yi magana kan harin  kwantan Bauna da mayakan Boko Haram suka kaimata.

 

Me magana da yawun sojin, Majo Janar John Enenche ya bayyana cewa sojoji 47 ne aka kashe musu lokacin kwantan baunan sannan kuma suma sun kashe wasu yan ta’addar har suka kwace musu mota daya.

 

Channelstv ta ruwaitoshi yana cewa yana jajantawa iyalan mamatan sannan kuma hukumar soji zata jajirce wajan ganin ta yi nasara a yakin.

 

 

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=hdlabarai.aplibwxOne Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *