fbpx
Wednesday, August 10
Shadow

Sojoji sun ceto mutane 22 da aka sace a jahohin Zamfara, da Katsina

Sojojin Najeriya da ke yaki da ‘yan bindiga da masu satar mutane a yankin arewa maso yamma sun dakile hare-haren’ yan ta’adda tare da kubutar da mutane 22 da aka yi garkuwa da su.

Sojojin sun kuma kwato makamai da alburusai a ayyukan da suke gudanarwa a  yankunan Jihohin Zamfara da Katsina.

Janaral Bernard Onyeuko, mukaddashin Daraktan yada labarai na tsaro, Shine ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Gusau ranar Juma’a.

Onyeuko ya sake nanata kudurin sojojin na Najeriya na kare rayuka da dukiyoyi, sannan ya bukaci mutane da su samar da sahihan bayanai game da mutanan da ba su yarda da su ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published.