fbpx
Sunday, February 28
Shadow

Sojoji sun fafata da ‘yan bindiga a Katsina, inda suka tilastawa yan bindigan guduwa

An ruwaito cewa sojojin na Najeriya sun fatattaki ‘yan ta’adda, wadanda suka kai hari kan al’ummomin Tashar Bawa da Sayau Dangado a karamar hukumar Sabuwa da ke jihar Katsina da rana tsaka a ranar Litinin.

 

Majiyoyi sun ce ‘yan fashin sun je garin Tashar Bawa da misalin karfe 10:15 na safe suka sace babura da dama da wasu abubuwa, ciki har da wayoyi.
Daga nan suka koma Sayau Dangado, inda suke shirin sace wasu mazauna garin, lokacin da sojojin suka isa kauyen.
An gano cewa ‘yan fashin, a kan ambaton sojojin, sun yi watsi da wasu kayayyakin da suka wawushe sannan suka tsere.
Kokarin tabbatar da faruwar lamarin daga Birged ta 17 na sojojin Nijeriya bai yi nasara ba saboda an tura binciken zuwa Hedikwatar Tsaro, Abuja.
Shi ma kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Katsina, SP Gambo Isah, ba a samu jin ta bakinsa ba saboda an ce yana halartar wani taro.
Haka kuma, ‘yan bindigar sun kuma yi garkuwa da mutum takwas a daren Litinin a kauyen Dugun Sambo da ke karamar hukumar Dandume ta jihar.
An ce ‘yan fashin sun far wa kauyen da misalin karfe 10 na dare.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *