fbpx
Wednesday, March 3
Shadow

Sojoji sun kashe mayakan Boko Haram 19 a Rann, tare da lalata motocin daukar bindigogin su

Sojojin Najeriya sun dakile wani hari da kungiyar Boko Haram ta kaiwa garin Rann a ranar Talata.
Sojojin sun kashe ‘yan ta’adda 19 kuma sun lalata motocin daukar bindiga biyar bayan kazamin artabun.
Rann sanannen gari ne a cikin karamar hukumar Kala Balge a jihar Borno.
Maharan sun afka wa yankin da misalin karfe 6 na yamma a kan manyan motocin daukar bindiga guda takwas, babura da dama sannan suka bude wuta kan ma’aikatan Brigade 3 a sansanin soja.
Wata majiya ta fada wa PRNigeria cewa bayan janyiwar dabara daga sansaninsu, sojoji sun kai wani mummunan hari ta sama da ta kasa kan ‘yan ta’addan.
Sojojin saman (ATF) da sojojin kasa sun tilastawa ‘yan ta’addan tserewa daga sansanin sojojin yayin da maharba sojoji suka yi musu kwanton-bauna.
“A yayin harin, an lalata manyan motoci biyar mallakar‘ yan ta’addan Boko Haram, ciki har da mutanen da ke ciki.
“An kashe ‘yan ta’adda da yawa a yayin yakin iska da hare-hare ta kasa da sojoji suka aiwatar.
“Akalla gawarwakin 19 daga cikin mayakan na Boko Haram sun cika wurin, tare da manyan bindigogin, baya ga wasu a cikin daji”, in ji majiyar.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *