Friday, May 29
Shadow

Sojoji sun kashe ‘yan Bindiga 29 tsakanin Zamfara, Katsina, Nasarawa Da Benue

Hedikwatar tsaro ta Najeriya ta bayyana cewa sojojin Sama a wani hari da suka kai tsakanin iyakokin Katsina da Zamfara a garin Nahuta-Doumborou ya kashe ‘yan ta’addar 27.

Ta kuma kara da cewa a Jihar Benue da Nasarawa kuma, Harin da suka kai a maboyar dan ta’addarnan da ake nema Ruwa a jallo, watau Gana ya myi sanadiyyar kashe ‘yan Bindiga 2 inda wasu ciki hadda Gana suka tsere da harbin bindiga a jikinsu, hakanan sojojin sun kama wasu ‘yan kabilar Bassa su 7 dake shirin kai hari kauyuka.

 

Sanarwar tace a jimlace sojojin sun yi nasarar kashe ‘yan ta’adda 29.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=hdlabarai.aplibwxLeave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *