Sojojin Najeriya sun sake kashe wata bataliyar ‘yan ta’addan Boko Haram 11 a kokarin da rundunar take na kakkabe ayyukan ‘yan kungiyar tada kayar baya dake a yankin Arewa Maso Gabas
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da aka fitar a Abuja a ranar Laraba ta Babban Jami’in Harkokin Watsa Labarai, Ma’aikatar Tsaro, Manjo Janar John Enenche, game da ayyukan rundunar sojojin Najeriya a ‘yan kwanakin da suka gabata.
Rundunar ta bayyana kwace makamai da bindiga kirar AK-47 tare da babur hadi da abubuwa masu fashewa.
A dai ‘yan kwanakin nan rundunar sojin Najeriya ta zafafa wajan kai farma ki ga masu tada kayar baya.