fbpx
Tuesday, March 28
Shadow

Sojoji sun kwace iko da kasar Zimbabuwe: Amma sunce ba juyin mulki zasu yi ba

Sojoji a kasar Zimbabuwe sun kwace iko da gidan talabijin na kasar sannan sun mamaye kan tituna a wani yunkuri da akewa kallon juyin mulkine, amma, a sanarwar da suka fitar, sunce ba juyin mulkine zasu yi ba, suna neman masu lafine da suka hana ruwa gudu a kasar dake zagaye da shugaban kasar, Robert Mugabe.

Sun kara da cewa da zarar sun kammala komai zai dawo yanda yake, kuma shugaban kasar da iyalanshi suna cikin koshin lafiya, suna samun kulawa yanda ya kamata.

Karanta wannan  Zababben Sanatan Nasarawa Ta Yamma Kenan Sanye Da Farin Kaya, Alaramma Ahmed Aliyu Wadada Yake Ja Wa Sheik Sabo Baki Yayin Tafsirin Ramadan Da Suke Gudanarwa A Yankin GRA Dake Garin Keffi, Jihar Nasarawa

Saidai wasu masu sharhi akan al’amuran kasar sun bayyana cewa wannan juyin mulkine, kawai sojojin basa so su bayyana hakane saboda sun san cewa Duniya ba zata basu goyon baya ba.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *