Sojojin Najeriya sun bayyana wasu daga cikin nasarorin da suka samu a baya bayan nan kan wasu ‘yan bindiga da ke yawo a yankin Arewa maso Yamma.
Sojoji sun kwato shanu 17 daga hannun barayin shanu a kauyen Dogon Ruwa. An dawo da shanun daga hannun wasu ‘yan fashin da suka yi watsi da su kuma suka gudu. Hutudole ya fahimci cewa hakan ya farine yayin da sojoji suka mamaye kauyen bayan samun bayanan ayyukan su daga majiyoyin amintattu.

A wata sanarwa da kakakin rundunar, Bernard Onyeuko ya sanyawa hannu, Hutudole ya samo muku cewa rundunar ta ce Operation Sahel Sanity sun karbe shanun tare da kama wasu da ake zargin ‘yan fashi da makami ne a‘ yan kwanakin da suka gabata.
“Babban hafsan sojojin, Laftanar Janar Tukur Yusufu Buratai ya yabawa sojojin bisa ga nasarar da suka samu, da kuma juriya da suka yi,” Onyeuko ya ce a cikin sanarwar sa.
“Ya gargadesu kar su huta game da yakin, Ya kuma kara tabbatar wa jama’ar yankin Arewa maso Yamma game da kudurin Najeriya na tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin da ke yankin. ”