fbpx
Wednesday, August 10
Shadow

Sojoji sun lakadawa ‘yan sanda dan banzan duka har insfeto ya mutu kan sunki gayara masu hanya su wuce a jihar Legas

Sojoji sun lakadawa jami’an ‘yan sanda guda biyu dan banzan duka inda har suka aika insfeto Monday Orukpe lahira.

A ranar laraba ne wannan lamarin ya faru a jihar Legas bayan da ‘yan sandan suka ki gyarawa sojojin hanya su wuce suka ce masu jira.

Wanda hakan yasa suka fusata suka fito suka dauke su suma tafi dasu bariki wanda a hanya suka lakada masu duka har insfeton ya fara shurawa.

Sun hanzarta kai shi asibiti amma duk da haka ranar alhamis ya bakunci lahira yayin da hukumar ‘yan sanda tace tana gudanar da bincike akan lamarin.

Leave a Reply

Your email address will not be published.